0

Gasar mai lakabi suna( FARAR ANIYA LAYA YPUTHS SOCCER FOOTBAL COMPETTITION) Anshiryatane domin kawo zaman lafiya da hadinkan matasa a wannan yankin karamar hukumar ta ikara a yayinda lokacin zabe ke karatowa a kokarinsa nakawo karshen bangar siyasa da kuma tada zaune tsaye atsakanin matasa musamman alokutan zabe.

Wannan gasa dai itace karo na farko wanda za’afara gudanarda ita a ranar 12/10/2022 afilin wasa na Ahmad Muhd makarfi dake tsakiayar garin Ikara idan Allah yakaimu,tuni dai kwamitin gudanar da gasar suka shirya tsaf domin fara wannan gasar.

Wasan farko dai zaikasancene tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Ikara Professional dakuma Ikara Super Star a babban filin wasan dake garin ikaran damisalin karfe hudu na Yammancin goben idan Allah yakaimu.

Anasaran shugaban karamar hukumar Ikara Dr Sadiq Salihu Ibrahim ne, zaibude gasar,haka kuma anasaran dukkanin daukacin manyan ‘yansiyasan da kananansu dake karamar hukumar kwata zasu kasance awurin domin ganin yadda zatakaya awannan rana.

Sani Dannata.
Tauraruwa TV
Shakallo.

Share
Go Top