00

Shugaban hukumar wasan kwallo kafa na jihar neja, kuma memba a hukumar wasan kwallon kafa na kasa NFF Alh Yusuf Fresh yace, baida masaniya da labarin dawata kafan watsa labarai na yanar gizo wacce ake kira da (insideglasshouse) dake watsawa cewar yana goyan bayan cigaban shugabancin hukumar karo na uku wanda shugaban hukumar na kasa Amaju Panick yake jagoranta.

Ahmed Fresh wanda yace yanzu lokacin magana akan waye zaici gaba da shugabantar hukumar baiyiba, abindake gabanmu yanzu shine ya zamuyi babbar kungiyar kwallon kafa ta kasa watau super eagle tasamu nasara awasan dazamuyi, dakuma kawo mata wasu hanyoyi na samun nasarori nan gaba.

Yakamata mutane su sani cewar Ahmad fresh ko Shehu Dikko basu da hukurimin dazasuce wai gawanda zai zama shugaba a wannan hukuma, tunda dokokin hukumar sunbada tsarin zabar shugaba, kuma dukkanin masu hakki acikin zaben sai sun amince kafin a sanko wanene zai jagoranci awannan hukuma.

Daga karshe Fresh yace jama’a suguji kama jita jita daga wasu jaridu marasa tabbacin labari, inda yabarranta kansa da wannan labarin kuma yace kanzan kuregene.

Sani Dannata
Taurauwa TV
Shakallo

Share

Post comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Go Top