00

Shahararriyar kungiyar Kwallon kafa dake garin Ikara watau Ikara soccer academy fc dake karamar hukumar Ikara, zata karbi bakuncin takwararta dake karamar hukumar makarfi watau Bayern Munich fc.

Wasan zaikasancene a ranar litini wanda yayi daidai da 03-07-2022 damisalin karfe hudu na yamma a babban filin wasa na Ahmed Muhammad Makarfi dake tsakiyar garin Ikaran.

Wasandai yazone adaidai lokacin da kungiyar ke kokarin ganin tayi wani gwaji na yanwasanta sabbabi dakuma tantance wadanda zasu waklici kungiyar agasarcin kofin Gwamnan jihar kaduna ajin matasa wanda kowace shekara ake gabatarwa afadin jihar, dayake karin haske dangane dawannan wasan, Maihorarda yan wasan kuma babban kochan kungiyar Coach Abdullahi Sani Ikara, yashaidawa manema labarai cewar wannan wasa wani sharefagene ko kuma gwajine ga yan wasan don ganin kwarewarsu dakuma cikakken lafiyarsu dontunkarar wannan babbar gasa dake gabansu.

Babban sakatarenn kungiyar Alh Sale Bala Ikara shima yayi tsokaci game da wasan, indayace yanada amanna cewar wasan zaikawatar ganin yadda gwanayen kungiyoyin suka shiryama wannan wasan sada zumunci, yakara dacewar babu tantama masu kallo zasuba idonsu abinci kuma zasu nishadantu da wannan wasa, daga karshe yayi fatan Allah yasa ayi wasa lafiya atashi, kuma Allah yamaida baki gida lafiya.

Sani Dannata
Taskar Wasanni Tauraruwa TV shakallo.

Share

Post comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Go Top