0

Mahimmin abun dubawa ga al’umma idan akazo maganar wakilici shine, wanene yakamata ya wakilceka? Kuma menene dalilinka nagoya masa baya? Kuma wani yakini kakeledashi Idan haryasami daman wakilcinka amajalisar wakilai?

Zandauki karamar hukumar Ikara amatsayin abin kwatance gameda wanda yadace yazama wakilinsu a majalisar jihar kaduna.

Mudauki dantakarar jam’iyar gwamnati Wanda takeci yanzu, akwai mahimman abubuwa dayakamata ace yasamarma karamar hukumar Wanda daga zauren majalisar yakamata yanemo sahalewar ‘yanmjlisun domin nuna kokarinsa ga al’ummar dayake wakilta, yayi kokari wurin kawo wasu ayyuka ga karamar hukumar, kamarsu gyarn hanyar janmarmara zuwa saulawa, kurmin kogi zuwa Dallawal dadai sauransu, amman abin tambaya anan shine, menene dalilin dayasa tun shekaru bakwai dayakwashe yanakan mulki baisamardasuba, sai yqnzu lokacinda yake ganin karshen wa’adun mulkinsu yazo? Idan muka lura, zamugane cewar datun baya yayi wadannan ayyuka datuni bawannan batun akeyi yqnzuba, amman rashin maida hankali garesu yakawoma wannan yankunan cibaya matuka ta fannin noma, tattalin arziki, neman ilmi dakuma harkokin kasuwanci.

A daya bangaren kuma shidantakarar jam’iyyar adawa ta PDP, wanda tsohon kamsilane sau biyu, kuma tsohon shugaban karamar hukumane sau biyu, kuma yayi ayyuka matukata wanda yqnzu haka anacin moriyarsu afadin karamar hukumar, irinsu, hanyoyi, ajujuwan karatu, kasuwanni na zamani, kananan asibitoci, sannan kuma ga bayar da tallafi dayayi ga dalibai domin karo karatu, sannan ga baiwa mata da maza, matasa da tsoffi tallafi domin kawar da talauci amatsakanin al’umma tun awancan lokacin.

Tau idan mukayi duba da idanuwan basira, cikin wadannan mutane wanene yadace ace munturashi domin yawakilcemu amajalisar kaduna domin kawo cigaban al’ummar wannan karamar hukuma?

Wadannan yantakara guda biyu daisune, Alh Abdulwahab Idris Kurmin Kogi na jam’iyyar APC, da kuma Alh Alasan Muhd Datti na jam’iyyar PDP.

Sani Dannata
Tauraruwa TV
Sha Kallo

Share
Go Top