Uncategorized

SIYOM FC ZATA KAFA TARIHI MAI DOGON ZAMANI

Kungiyar kwallon kafa mai suna SIYOM FC international kaduna, kungiyace dake dillanci, siyarwa, siye dakuma tallafama kananan matasan yankwallon kafa sama musu kungiyo ciki da wajen kasarnan, domin morema irin basirar da Allah yabasu.

Abin alfaharine na samun irin wannan kugiya akowane kasa ko gari domin kawoma matasa sana’a da kawar da zaman banza tsakanin al’umma, wannan kalamin sunfitone daga bakin Sir David wanda yaziyarci wannan kungiya tun daga kasar Birtaniya domin gabatar da wani sharhi kan karama yanwasa dakuma shuwagabanninsu sanin yadda ake gudanar harkokin wasanni akasashen duniya domin gagayya dasauran manya manyan kungiyoyi.

Mr David ya yabi shugaban kungiyar SIYOM FC international Academy Malam Salisu Isah dacewar mutum ne maikokari, hazaka, da basira gayadda yake bada gudunmawan kawo cigaban matasa ta kowacce hanya domin kawar da zaman banza ga matasa tahanyar sama musu sana’a abangaren wasan kwallon kafa, inda mr David yace yakamata gwabnati tashigo cikin wannan tsarin domin tallafama wannan bawan Allah ganin yacimma burinsa na habaka harkokin wasanni gida da waje.

Daga karshe mr David Yayi godiya da irin karamcin da yasamu alokacin zuwansa kaduna najeriya domin bada lacca ga mahalarta taron don sanin sabbabbin hanyoyin kawo cigaba da harkokin wasanni a sauran kasashen duniya.

Sani Dannata
Tauraruwa TV
Sha kallo.

Related Articles

Back to top button