00

Kungiyar kwallon kafa ta SIYOM FC dake birnin kaduna, kuma kungiya ta farko data fara daukar farar fata amatsayin mai horaswa, kuma tana dibar yaran ne tahanayar gwaji dakuma duba masu fasaha da kwazo wurin sarrafa kwallon kafa, domin sama musu gurbi ko kungiyoyin wasa afadin duniya.

Shugaban kungiyar Alh Salisu yace itafa wannan kungiya haryanzu kofarta abude take ga duk mai sha’awar zuba jari a wannan kungiya domin habaka harkokin wasanni na ajin matasa.

Salisu yakara dacewa zuwa yanzu akalla yara kusan gudu ashirin ne suka sami kungiyoyi daban daban a fadin duniyan nan domin wasan kwallon kafa, yakuma yakawo mai horaswanne farar fata domin karama yaran hazaka da kuma basu dubarun yadda ake wasan kwallon kafan na zamani akasashen turai dama sauran kasahen duniya.

Kungiyar SIYOM tanada akallah yan wasan fiye da guda hamsin wadanda suke karbar horo, kuma kungiyace datake dauke da yara matasa daga ko ina afadin kasarnan wadanda sukaci jarabawar gwaji da aka gabatar domin tantance wadanda suka dace da wannan kungiya.

Munada kwararrun likitoci, masu kulada yan wasa, kyakkayawan makwancin yawasan, wadataccen kayayyakin buga wasan, tare da filin wasa mai ingaci dominjin dadin yanwasanmu, inji Alh Salisu shugaban kungiyar.

Sani Dannata
Taskar Wasanni
Tauraruwa TV sha kallo.

Share

Post comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Go Top