0

Ayayinda lokacin zaben shuwagabannin kungiyar marubuta labarin wasanni ta kasa (SWAN)ke karatowa, masana da masu bibiyar harkokin wasanni sunata tattaunawa tareda dubi kowanene yakamata yajagoranci kungiyar ayayin zaben dake tafe.

Kashi chasa’in cikin dari na nuna cewa babu maimagartar dayadace ace yagoranci kungiyar kamar Mal. Rilwan Idris Malikawa Garu, wanda kowa yasanshi afagen wasanni shekaru da dama yana bada gudunmawa wurin habaka harkar wasannin tundaga karkara haryazuwa mataki kasa baki daya.

Idan mukaduba, Malikawa tsohon danwasan kwallon kafa ne, tsohon maihorarwa ne,kuma gogaggen Dan jaridane musamman abangaren wasanni,tsobon shigaban kungiyar marubuta labarin wasanni na jihar kano,tsohon maisharshi ne akan wasanni gida da waje, kuma jagorane dayakeda nagarta,ilmi,natsuwa,tausayi,da tunanin yadda za’asami cigaba aduk abinda yasa agaba.

Zaben Mal. Rilwan Idris Malikawa Garu amatsayin shugaban kungiyar marubuta labarin wasanni ta kasa, zai samarda hadin kai,zaman lafiya,kaunar juna da kuma dunkulewar kungiyar amatsayinta na uwa da uba daya, donhaka yakamata ace dukkan maikishin kungiyar dasan cigabanta yabada tashi gudunmawar ganin malikawa yakai ga nasara.

Sani Dannata
Tauraruwa TV
Sha kallo.

Share
Go Top