0

Tsohon sakataren ilmi na karamar hukumar Ikara jihar kaduna, Alh Dahiru Sule yayi alkawarin jagorantar mata da matasa na akwatunan unguwar akawu da makera a mazabar ikara cikin gaskiya, cika alkawari da rikon amana, Dahiru sule yayi wannan alkawarinne alokacin dayake gabatar da bayanansa ataron membobin masu kada kuru’ a wadannan akwatunan, hakazalika yayi Allah wadai da iron halinda yaga al’umma keciki na kunci, talauci, da rashin aikiyi ga matasa, inda yabayyana hakan amatsayin rashin tausayi dacin amanar al’umma da gwamnati maici ta APC ayanzu takawo akasarnan.

Alh Dahiru Sule yace yakamata al’umma suyima jam’iyar PDP adalci dubada, yadda ta wadatar da al’umma tafanni daban da badan, wanda yace shi karan kanshi yaraba takardun aikinyi na koyarwa ama’aikatarsa ta ilmi misalin guda dari ayayinda yake shugabantar ma’aikatar a karamar hukumar.

Tsohon sakataren ilmin yajagoranci mai’aikatar ta kimanin shekaru takwas akarkashin mulkin jam’iyar PDP, daga karshe yahori al’umma dasu kara baiwa jam’iyar PDP din dama domin dawomusu da ingantacciyar rayuwa kamar yadda sukayi awancan zamanin.

Daga karshe al’ummar akwatunan mata da matasan sunyi alkawarin baiwa jam’iyar PDP kuru’unsu kimanin dubu hudu, tundaga sama har kasa.

Sani Dannata
Tauraruwa TV
Sha kallo

Share
Go Top