0

Shugaban kwamitin social media na kamfen dinin shugaban kasa da gwamnan jihar kaduna karkashin jam’iyar PDP Mr Victor Bobai yayi kira ga daukacin membobin kungiyar dasu zama masu aiki tukuru babu gajiyawa domin ganin jam’iyar tasami nasarar zabe mai tunkarowa.

Mr Bobai yayi wannan kirane alokacin dayake bayani ga membobin kungiyar gameda irin nauyin dayataru akansu, wanda yace yanzu lokacine dakashi chasa’in cikin al’ummar kasarnan suna amfani da social media ta hanyar samun labaru masu amfani, danhaka yace yazama dole kwamitin yayi duk maiyiwuwa ganin ya nusarda al’ummar jahar kaduna da kasa baki daya irin alfanun jam’iyar PDP tasamar doncigaban kasa baki daya.

Daga karshe dai shugaban kwamitin yayi fatanan samun nasara ga jam’iyar tasu ta PDP ajiha da kasa bakidaya,shugaban kwamitin kanfen na social media Victor Bobai yayi kumafatan hadinkan membobin da ‘ya’yan jam’iyar PDP baki daya,domin ayi aiki tukuru.

Sani Dannata
Tauraruwa TV
Sha kallo

Share
Go Top