0

Dukkan shirye shiryenmu sunkammala donganin anfara gabatar da gasar Dala hard court tennis ta kasa anan kano,wannan kalamin sunfitone daga bakin babban daraktan kula da harkokin tennis din na jihar kano Alh Yusuf Datti yayin ganawa da manema labarai ayau dangane da sanardasu irin shiryen shiryen fara gasar ta bana anan kano.

Alh Yusuf Yace duk da karin farashin kayayyekin gabatarda gasar, hukumar tennis ta kasa ta sahalema hukumar tanan kano kudi kimainin miliyan asirin da bakwai donganin ankammala gasar cikin nasara da tsari maikyau,Alh Yusuf yakara dacewar sinbaiwa hukumar shawarar gayyato ‘yanwasan tennis na kasa misalin asirin daga maza, dakuma goma daga bangaren mata domin ganin gasar tabana tayi armashi.

Zadai afara gasar share fage a ranar 11 ga watan nowanba na wannan shekarar zuwa 13 ga watan nowanban, daganan za’acigaba da gasar daga ranar 14 gawatan nowanban wannan shekarar,kamar yadda babban daraktan yabayyana hakan ga ‘yanjaridu,haka kuma anasara aranar rufe gasar maigirma mataimakin gwamnan jihar kano zaikasance babban bako awurin rufe gasar.

Duk wanda yazo na daya abangaren maza agasar Dala hard court tennis championship din zaitashi da makudan kudi har naira miliyan daya,sai abangaren mata kuma na daya zatasami dubu dari shida,kuma anasaran kamfanonin Dangote,fidility bank,first bank of nigeria,wacot limited da daisauran masu ruwa datsaki aharkàr nadaukar nauyin Dala hard court championship tennis zasu bada nasu gudunmawar kamar yadda akasaba domin ganin gasar tayi armashi ga mahalarta.

Sani Dannata
Tauraruwa TV
Shakallo.

Share
Go Top