0

Shugaban kamfanin buga ledar yashaidawa mahalarta taron cewar, duba dayadda irin gudunmawar da MD na Tauraruwa TV kebadawa musamman tafannin habaka harshen hausa da al’adun hausa aduniya yanuna karara cewar yachanchanci ayaba masa, wannan shine dalilinmu nabashi wannan kyauta na shugaban gidan Telebijin na satilat masu magana da harshen hausa dayafi kowa gwazo a wannan sheraka.

Shugaban gidan buga wannan Leda yabada wannan kyautarce a lokacinda yashirya wani biki domin bada kyaututtuka ga mawaka,marubuta,dakuma masu bada gudunmawa na daukaka harshen hausa afadin duniya, taron yagudnane anan garin kano, duba dayadda akema garin kirari da tushen hausa.

Haka kuma daya daga cikin ma’aikatan gidan Tauraruwa TV, watau Daraktan daukar hoto daku hada hotunan Malam Abdurrahman Abdullahi Fagge nacikin wadanda aka baiwa kyautar, wanda yalashe kyautar gwarzon mai’iya hada hutuna da tattacesu a wannan shekara wanda kamfanin yabashi.

Daga karshe anhori wadanda akabaiwa kyaututtukan dasu kara karfi dacigaba da daukaka harshen hausa aduniya bakidaya.

Sani Dannata
Tauraruwa TV
Sha kallo.

Share
Go Top