00

Shugaban kungiyar kwallon kafa na Kano pillars kuma shugaban ma’aikatar wasanni na jihar kano Alh Ibrahim Galadima yace haryazuwa yanzu babu wani mataki da gwamnati ta dauka dangane da hukuncin da hukumar wasanni ta kasa ta dauka agame da yadda suka cire maki uku tare dacin kungiyar kano pillars tarar miliyoyin kudi akan yadda tsohon shugabanta Alh Shu’aibu Jambul yadaki maitaimakin alkalin wasa a ranar da kungiyar tayi wasa da kungiyar kwallon kafa ta Dakada fc anan filin wasa na Sani Abacha dake kofar a jihar kanon dabon.

Shugaban yakara dacewar saina tattara dukkan bayanai na wuri guda natura ga gwamnati, sannan gwamnati tagama nata tunanin tare da duba yadda hukuncin yake, sannan tasan matakinda zata dauka agame da wannan hukuncin da akayiwa kungiyar ta kano pillars din, shugaban yayi wannan bayanine a lokacinda kungiyar marubuta labarin wasanni reshen jihar kano suka kai masa ziyara a ofishinsa donjin halinda kungiyar takeciki game da hukuncin da hukumar kula da harkokin wasanni takasa tayima kungiyar.

Sani Dannata
Tauraruwa TV
Sha kallo.

Share

Post comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Go Top