00

Yayin dayake bayani kafin bada wannan kyautar shugaban wannan kungiya Malam Usman Aminu suleman,yace sunbada wannan kyautar ne ga shugaban gidan telebijin na Tauraruwa TV sha kallo Alh Muhd Salis don ganin yadda yake bada gudunmawa ga baiyana alkairin da sarkin Kanon na sha hudun khalifa Sununsi Lamido Sunusi yayi lokacin yana Sarkin Kanon, yakuma kara dacewa hakika mai martaba na godiya da irin wannan gudunmawa dasuke samu daga gidan TV.

Dayake karbar kyautar shugaban gidan Telebijin na Tauraruwan Alh Muhd Salis yace tsari, tausayi, tunani maikyau, hade tausayi irin na khalifa muhd Sunusi lamisunusi yasa sukaga yadace sucigaba da fadakar da mutane irin gudunmawar dayabada alokacin yana gadan sarautar kanon, yace wannan aikin yazo daidai da irin tsarin gidan Telebijin din Tauraruwane danhaka yaga dacewar bada gudunmawarsa awannan bagaren.

Daga karshe shugaban yayi godiya ga wannan kungiya, saikuma yayi kira ga sauran kungiyoyi dasuyi koyi da irin wannan kungiya don karama shugabannin karfin guiwa ganin sunyi bar abin koyi ga al’umma aduk lokacin dasuka tsinci kansu a wata dama dasuka samu kamar yadda Khalifa Sunusi Lamido Sunusin yayi wand ayanzu haka sama da mutum miliyan biyu suke amfana da irin abin alkairinda yabari alokacin mulkinsa.

Sani Dannata
Tauraruwa TV
Shakallo

Share

Post comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Go Top