0

Daya daga cikin membobin kwamitin kamfen zabe na social Media a jam’iyar PDP jihar kaduna, Dr Bege Sa’id Mark yace dantakarar gwamnan jihar kaduna karkashin jam’iyar PDP Rt. Hon. Isah Ashiru kudan hazikine dazai al’ummar jihar kaduna tudun muntsira idanhar akazabeshi amatsayin gwamnan jihar azabe maizuwa.

Dr Bege yayi wannan kalamine yayinda yake jawo hankalin al’ummar jihar kaduna alokacinda zabe ke karatowa, yace matukar mukayi amfani da kur’iar da mukeda ita awurin zabe,kumq muka tabbata muntsaya domin kare kuru’unmu a yayin zaben, tau lallai zamu kori kungiyar APC daga gidan gwamnatin jihar kaduna,domin dawo da jam’iyar dake da tausayi,taimakon al’umma,raya kasa,dakuma samamar mana aikinyi ga mata da matasa.

Yakara dacewar hakika kungiyar APC tashigarda al’ummar jihar kaduna cikin talauci,kuncin rayuwa,yunwa da rashin aikinyi, gashi kuma taraba mutanen jihar kaduna fiye da dubu goma aikinyi, danhaka yazama wajibi murama biki.

Daga karshe yayi kira ga daukacin membobin social media na kwamitin yakin neman zaben jam’iyar PDP na jihar kadunan, dasu zama hazikai,masu kokari da fadakarda al’umma halinda akeciki ayanzu, domin kawo sauyi mai ma’ana azabe maizuwa.

Sani Dannata
Tauraruwa TV
Sha kallo

Share
Go Top