00

Shugaban Kungiyar matasan jam’iyar PDP na karamar hukumar Ikara, wacce akasani da Ikara PDP Youths Ambassadors, Malam Nazifi Abdullahi wanda akasani da (Ikara Son), yayi kira ga al’ummar karamar hukumar Ikara dasu zabi Hon. Alasan Muhd Datti amatsayin dan majalisar wakilai mai wakiltar Karamar hukumar Ikara akakar zabe mai zuwa.

Yayin wwannan kira shugaban kungiyar na karamar hukumar Ikara, yace duba da yadda karamar hukumar ikaran tazama tabaya afanni morar ribar dimokridiyya agwabnati maici sabida irin rashin wakilci na gari a majalisar jiha, yace bai kamata ace tsohuwar karamar hukuma irinta Ikara, amman tarasa wakilci ingantaccen a majalisar jihar domin kawo mahimman abubuwa ga karamar hukumar.

Yakara dacewar lokaci yayi da al’ummar karamar hukumar ikara dazasuyi karatun tanatsu domin nemama kansu mafita ta hanyar zaben wakili na gari wanda shine Alh Alasan Muhd Datti ikara, wanda yace Alasan din yayi kansila, yayi shugaban karamar hukuma, haka kuma yayi mai baiwa gwamna shawara, yayi sakataren jam’iya, yana kuma da kwarewa a fannin siyasa da harkokin siyasa, inda yabaiyana Alh Alasan Muhd Datti amatsayin wanda yasan halinda al’ummar karamar hukumarsa ta ikara keciki domin shida iyalanshi zaune suke acikin garin ikara, wanda yace hakan na nuni ga irin kauna hade da nuna soyayyah ga al’umma.

Daga karshe yayi kira ga dukkanin maikishin karamar hukumar Ikaran, dasuzo subada tasu gudunmawar ganin dantarar nasu yakaiga nasara azaben dake tafe.

Sani Dannata
Tauraruwa TV shakallo

Share

Post comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Go Top