0

Duba da yadda siyasar najeriya take ciki musamman nazuwan waadanda basuda ilmin siyasa,yakawo cibaya ga harkokin siyasa takowane fanni a najeriya,muduba yadda wasu tsirarin mutane sukamaida siyasa tamkar wani fage na cinzarafi komaida martani, ko kuma amfani da wata dama namuzguna mutane domin biyan bukatunkansu.

Mudawo karamar hukumar Ikara wacce tana daya dagacikin tsoffin kananan hukumomi a najeriya, amman hakan baisa wasu dagacikin ‘yansiyasar karamar hukumar yima kansu karatun tanatsuba akan yadda yakamata su jagoranci al’ummar karamar hukumarba.

Zan dauki Alh Alasan Muhd Datti, wanda shine Sarkin Yaki Ikara, kuma dantakarar kujerar majalisar jihar kaduna a karkashin jam’iyar PDP a shekara maizuwa,tsohon kamsila a jam’iyar DPM,tsohon kamsila kuma a jam’iyar PDP,tsohon Sakatare na Karamar hukumar Ikara a jam’iyar PDP,tsohon shugaban karamar hukumar ikara na ruko,tshon zababben shugaban karamar hukumar Ikara,tsohon maibaiwa Gwamna shawara,ayanzu kuma dantakarar majalisar jihar kaduna.

Muduba wadannan mukamai dayarike bisa fannin siyasa, shin kai wannan duk basu gamshekaba cewar lallai ilmin siyasa ya’isheshi yawakilcekaba?kanada wanda yafishine batun sanin mulkin siyasa ko wakilcina siyasa? Tau kai ina naka gwanin yarike kafin zuwansa wannan matsayi? Kuma wani irin rawa yataka ganin jam’iyarka tasamu dinbin magoya baya kamar yadda Alh Alasan Muhd Datti yayima jam’iyarsa? shidai Hon. Alasan dukkan mukaman dayarike acikin garin ikara yake zaune tare da al’ummarsa, domin gani, dajin halinda kowa yakeciki, kuma yana bada gudunmawa ta jaje, kota murna ga duk wanda wani abu yashafeshi batareda nuna bambancin siyasaba, tau maiyin wannan shine zaka hadashi da wanda yakai shekaru talatin ba agarin yake zauneba, asalima saida yadawo neman shugabancin siyasane wasu mutane suka nunama al’umma kowaneneshi, kashi 90 cikin al’ummar kaunyensu basusanshiba.

Wannan wani tsokacine dayakamata ace al’ummar karamar Hukumar Ikara sunyi dubi dakuma fahimtar tare danemo hanyar mafita ga al’umma domin zakulo wanda yasan damuwarmu kuma yake tare dasu komai ruwa,komai rana domin ganin sunsami cigaba dakuma cinribar dimokradiyya.

Sani Dannata
Tauraruwa TV
Sha Kallo

Share
Go Top