00

MD na Tauraruwa yayi wannan kalamine a lokacinda gidauniyar habbaka nasarorinda sarkin kano na 14 Sunusi Lamido Sunusi suka bashi lambar yabo ta girmamawa.

Nayi imani taimakon mutane shine hanya daya tilo dazata kawo cigaba ga al’umma tare darage radadin talaucin dake damun mutane awannan lokaci, kuma ina amfani da wannan damar danake da ita wurin taimakon masu karamin karfi ganin sunsami sauki na rashindake damunsu, inji Alh Muhd Salis MD Tauraruwa Tv.

A duk lokacinda naga wani mutum na cikin kunci narashi musamman magidanci nakanji kamar nine awannan hali, dan haka nasanyama zuciyata cewar zanyi duk yadda zanyi dakuma karfinda Allah yabani daidai gwargwado ganin nafitarda masu bukata cikin halinda suka tsinci kansu.

Daga karshe yayi kira ga al’umma musamman masu karfi da iko ahannunsu dasurika taimaka al’umma mabukata domin ganin ankawo mayuwacin halinda al’umma keciki na matsanacin talauci, wanda yace yana daya dagacikin abindake kawo rashin tsaro dakuma tabarbarewar al’umma musamman matasa awannan lokacin, MD yayi addu’ar Allah yakawo karshen tashe tashen hankula dakuma sace sacen al’umma dske faruwa a wannan kasa tamu mai albarka.

Sani Dannata
Tauraruwa TV
Shakallo

Share

Post comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Go Top