Uncategorized

ATIKU NE MAI CIN KWALLON, NI KUMA MAI TSARON GIDAN BAYA- GWAMNA FINTIRI________Sani Dannata

An gudanar da taron gangamin karbar mutane daga jam’iyar APC mai mulki zuwa jam’iyar PDP fiye da dubu goma, wanda yagudana a filin taro na Ribado dake tsakiyar garin Yolan jihar adamawa.

Related Articles

Gwamna jihar adamawa Alh Umar Fintiri yace Alh Atiku Abubakar tshon mataimakin shugaban kasar najeriya shine danwasa maicin kwallo, shi kuma yana baya yanamasa tsaro dan kada wani yayi masa badaidaiba agidansa, yakara dacewar Atiku Abubakar hazikin mutum ne kuma masani akan harkokin mulki da kasuwanci, wanda yace zai iya taimakawa wurin ganin najeriya tafita daga cikin halindata tsinci kanta aciki na rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki, Gwamnan yakara dacewar lokaci dayakamata yan najeriya suyi karatun tanatsu domin zaben Atiku abubakar zai zami alkairi garesu.

Anasa jawabin Tsohon mataimakin shugaban kasan, kuma dan takaran shugaban kasa a jam’iyar PDP Alh Atiku Abubakar yace duk dai ba lokacin Kamfen bane, amman baiwa Gwamna fintiri daman ta biyu azabe mai zuwa zai haifarmada jihar da mai ido, inda yakira Gwamna fintiri amatsayin bawan al’ummarsa kuma mai burin ganin jihar adamawa ta kerema sa’o’inta ta fannin more rayuwa da tattalin arzikin kasa, yakara dacewa tunda siyasa ta dawo ba’ayi Gwamnan dayayi abinda Fintir yayi a jiharba, yace gaskiya ya chanchanci yabo dakuma karin lokacin domin kammala aikin dayafara.

Daga karshe dai ankarbi alkallah mutane fiye da dubu goma daga jam’iya mai mulki ta APC zuwa PDP wanda yahada jihohin arewa masu gabas baki daya, daga nanne shugaban jam’iyar PDP na kasa Mr Ayu yace lokaci yayi na dawowar jam’iyar PDP kan mulki, yace yan najeriya suje sukarbo katukan zabensu domin shirin korar mutanenda suka maida yan najeriya bayi da kuma rashin kare rayukansu da dukiyoyinsu.

Sani Dannata
Tauraruwa TV sha
Kallo.
Daga Yola Jihar
Adamawa.

Related Articles

Back to top button