00
Alh Rilwanu Idris Malikawa Garu.
Dagacin Malikawa Garu

Alh Rilwanu Idris Malikawa Garu wanda sananne ne kuma dan jarida dake aiki da aiki a gidan radiyan jihar kano bangaren wasanni, tsohon dan wasan kwallon kafa, tsohon mai horaswa, tsohon shugaban kungiyar marubuta labarin wasanni ta jihar kano, kuma mataimakin shugaban kungiyar marubuta labarin wasanni reshen arewa maso yamma, kuma babban mai sharshin harkokin wasanni a najeriya da sauran kasashen africa baki daya.

A ranar ashirin da daya ga watan yuli shekara ta dubu biyu da ashirin daya(21-07-2021)mai martaba Sarkin Bichi kuma dan sarki Ado Bayero yanadashi amatsayin dagacin garin malikawa garu, wanda yanzu haka yana da shekaru biyu akan gadan wannan masarauta.

Abisa wannan ne al’ummar garin malikawa garu suketa murna dafatan Allah yakawa dagaci lafiya danisan kwana masu albarka.

Al’ummar garin malikawa garu sunce Alh Rilwanu Idris malikawa garu mutum ne mai sanin daraja da kuma mutumta dan adam, gashi da tunanin daku kokarin garin yasasanta al’ummarsa dakuma kawo musu cigaba wurin tattalin arziki dakuma kula da ilmi, da zaman tare, hardama hakuri da juna domin samun zaman lafiya da cigaban masarautarsu.

Al’ummar sunyi kira ga sauran dagatocin masarautar Bichi da kanon baki daya dasu zama masu koyi da salo dakuma irin halayen dagacin garin malikawa garu, inda sukace ya chanchi abin koyi ga sauran takwarorinsa.

Daga karshe sunyi addu’ar Allah yakarama dagacin nasu lafiya, kwarin guiwa, hakuri, cigaba, dakuma karin tattalin arziki da nisan kwana masu albarka.

Sani Dannata
Tauraruwa TV
Sha kallo.

Share

Post comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Go Top