0

Shugaban jam’iyar PDP na karamar hukumar Ikara Alh, Idris Yakubu maitaki yabayyana hakan, yayin wata ganawa dayayi amazabar Ikaran dake tsakaiyar garin, shugaban yabayyana cewar dubada irin gogewar Alh Alasan muhd Datti dayake da ita a siyasa, itace tabashi damar lashe zaben fidda gwani na jam’iyar PDP wanda yabata domin yarikema jam’iyar takarar zama danmajalisa mai wakiltan karamar hukumar ta ikara amajalisar jihar kaduna akakar zabe maizuwa.

Alh Idi maitaki yakara dacewar Allah yahorema Alasan datti, zurfin tunani,ilmin siyasa,zama da mutane lafiya,kishin karamar hukumarsa da al’ummarsa bakidaya,don haka yake kira ga daukacin al’ummar karamar hukumar ta Ikara da fito kansu da kwarkwatarsu alokacin zabe suzabi Alh, Alasan Muhd Datti amatsayin wakilinsu n majalisar jihar kaduna a zabe mai zuwa.

Hon. Alasan Muhd Datti tsohon kamsila sau biyu,tsohon sakataren jam’iyar PDP na karamar hukumar Ikara,kuma tsohon shugaban karamar hukumar, saboda haka yanada gogewa akan mulki da shugabanci musamman na siyasa, wanda wata damace zatayi masa jagoranci har idanyasami zama danmajalisa.

Sani Dannata
Tautatuwa TV
Sha kallo.

Share
Go Top